Labarai
Muna buƙatar samun harajin sama da Tiriliyan 10 a 2022 – FIRS
Hukumar tattara haraji ta ƙasa FIRS ta yi hasashen samar da naira tiriliyan goma da biliyan ɗaya ta hanyar karɓar kuɗaɗen shiga a shekarar 2022.
Shugaban hukumar Muhammad Nami me ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin ƙudi a Abuja.
Hukumar ta shirya taron jin ra’ayoyin jama’a ƙarkashin kwamitin da ta kafa game da tsarin yadda za a samu matsakaicin kudaden shiga a shekarar 2022 zuwa 2024.
Ya ce, Naira tiriliyan goma da biliyan ɗaya za a samar da su ne ta hanyar kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ta ke hasashen samu a shekarar 2022.
You must be logged in to post a comment Login