Labarai
Muna bukatar gwamnatin Kano ta soke jarrabawar Qualifying – PTA
Ƙungiyar iyaye da malaman makaranta ta ƙasa shiyyar Kano PTA, ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta soke ci gaba da rubuta jarrabawar Qualifying baki-ɗaya.
Shugaban ƙungiyar Malam Sani Salisu Dan-Hassan ne ya buƙaci hakan a yau yayin da shugabannin ƙungiyar suka ziyarci zauren majalisar dokokin Kano domin amsa gayyatar da kwamitin wucin-gadi da majalisar ta kafa kan faɗuwa a jarrabawar ya aike musu.
Ya ce akwai buƙatar gwamnatin Kano ta soke rubuta jarrabawar ta Qualifying tunda har gwamnatin ta sanar da cewa ilimi kyauta ne, amma gaza cin jarrabawar na sanya wasu daga cikin ɗaliban ba sa iya biya.
A na ta bangaren kungiyar shugabannin makarantun sakandaren jihar Kano ANCOPS ta bakin shugabanta Malam Safiyanu Na-Abba, ya bayyana rashin isassun malamai tare da wasu daga cikin matsalolin da ke janyo faduwa a jarrabawar.
Shi kuwa mataimakin shugaban majalisar Alhaji Hamisu Ibrahim Chidari, cewa ya yi kungiyar ta tattauna muhimman batutuwa da dama da su, kuma za ta yi amfani da su cikin rahoton da za ta gabatar a zauren majalisar.
Wakilinmu na majalisar dokokin ta Kano Auwal Hassan Fagge, ya rawaito cewa ziyarar kungiyoyin biyu wani bangare ne na ci gaba da aikin da kwamitin na mutum bakwai ke yi domin lalubo hanyoyin kawo karshen faduwa a jarrabawar.
You must be logged in to post a comment Login