Labarai
Muna bukatar Karin albashi ba nazarin albashi ba- Ngige
Minintan kwadago da ayyukan yi Dr Chris Ngige ya ce har kawo yanzu gwamnatin tarayya taki aiwatar da sabon tsari na biyan mafi karancin albashi na naira dubu talati ga ma’aikatan kasar nan.
Ministan ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da shugaban kungiyar ma’aikata Timothy Olawale a yayin da ya jagoranci yan kungiyar sa zuwa ofisn ministan a ofishinsa a jiya.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan kafin shiga tattaunawar fahimta tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ta kwadago, bayan da ta bayyana shiga yajin aiki muddin gwamnatin tarayya taki amincewa da tabbatar da Karin albashin.
Dr Chris Ngige ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti da zai sake duba batun mafi karancin albashi da ba zai gaza naira dubu talatin ba , wanda ake so ya fara aiki a shekara ta 2020, inda ya kara da cewa kasafin kudin gwamnati ya karu daga fiye da tiriliyan 1 zuwa fiye da tiriliyan 3 tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2020.
Amma har kawo yanzu an gaza tsayar da matsaya dangane da mafi karancin albashi ma’aikata.
Ya ce a halin yanzu babban abu mafi muhimmanci dai shine batun Karin albashin , ya ce shugaba Muhammadu Buhari dai ya sanya hannu ne kan batun albashin tun a ranar 18 ga Afrirun wannan shekara, tun daga wannan rana batun Karin albashi ya kamata ya fara aiki.