Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna cikin halin fargaba – Mutanen Maru

Published

on

Rahotanni daga garin Kadauri a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara na cewa, wasu ƴan bindiga sun hallaka mutane tara, tare da jikkata wasu da dama.

Ƴan bindigar sun kuma yi awon gaba da dabbobi a garin, kamar yadda wani mazaunin garin ya shaidawa wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaɓa cewa bayan maharan sun shigo kauyen sai suka buɗe wuta a kan mutane.

Wakilin na mu ya tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda na jihar ta Zamfara SP. Shehu Muhammad wanda ya ce zai yi magana da kwamishinan ƴan sandan jihar daga bisani zai tuntuɓeshi, amma dai har kawo lokacin da mu ke haɗa wannan labari bai tuntuɓe shi ba, kuma ko da ya ƙara kiransa bai ɗaga wayar ba.

Jihar Zamfara dai na cikin jihohin da ake samun yawaitar rahotannin hare-haren ƴan ta’adda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!