Labarai
Muna cikin tashin hankali biyo bayan cikar wa’adin da ‘yan bindiga don karbo ‘yan uwan Nabeeha
Iyalan budurwar nan, Nabeeha Al-Kadriyar da a baya-bayan nan ta rasa ranta a hannun yan bindiga sun ce suna cikin tashin hankali saboda karewar wa’adin biyan kudin fansar da masu garkuwar suka bukaci a biya.
Asiya Adamu, wadda ta yi magana da BBC a madadin iyalan yan matan, ta ce a yanzu haka suna sauraron kiran waya ne daga ƴan bindigan domin sanin mataki na gaba.
Ta ce a halin yanzu iyalan sun yi bakin abin da za su iya, to amma suna jiran umarni daga masu garkuwa da yaran.
Ta ce: “Hankalin kowa a tashe yake, muna jira, muna kewar su. Kawai muna son mu ga sun dawo,” in ji Asiya.
Ta ce a duk lokacin da yan bindigar suka tuntubi iyalan yan matan suna hada su da iyayensu a waya su yi magana don su fada musu halin da suke ciki tare da neman su gaggauta biyan kudin fansar da masu garkuwa da su suka nema.
A ranar 2 ga watan Janairu ne yan bindigar suka sace Nabeeha da mahaifinta tare da yan uwanta biyar – Nazeera (20), Najeeba (23) sai tagwaye Ajeeba da Aneesa (13) da Mardiyya daga yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya inda kuma suka nemi a biya su maƙudan miliyoyi, waɗanda iyalan suka ce sun fi ƙarfinsu.
Sai dai sun saki mahaifin yan matan domin ya je a hada kudin fansar yayansa amma kafin a kai ga hada kudin ne kuma Nabeeha ta rasa ranta a hannun yan bindigar daga bisani suka kara adadin kudin fansar.
Asiya ta ce suna kewar yan matan kuma iyalan na ci gaba da addu’a domin neman mafita.
Labarin sace yan matan dai ya karade shafukan sada zumunta inda kungiyoyi da fitattun yan siyasa kamar Atiku Abubakar da Sheikh Isa Ali Pantami da wasu masu amfani da shafukan sada zumuntar suka yi ta nuna rashin jin dadi kan yadda matsalar sace-sacen jama’a ke kara kazancewa a Najeriya.
Ita ma mai dakin shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta bayyana yadda labarin mutuwar Nabeeha ya girgizata inda ta yi kira ga jami’an tsaro su kara kaimi domin ganin an kubutar da ragowar yan matan da ke hannun yan bindigar.
You must be logged in to post a comment Login