Labarai
Muna zargin anyi mana rubda ciki da tallafin da gwamnati ta bamu-Yan Kasuwar Kurmi
Yan kasuwar Kurmi a Jihar Kano wadanda suka gamu da ibtila’in gobara a kwanakin baya, sun zargi shugabancin kasuwar da yin rub da ciki da tallafin da gwamnati ta basu na naira Miliyan 50.
Yan kasuwar dai suna zargin kwamitin da gwamna ya samar na basu tallafin milyan 50 ya hada kai da shugabancin kasuwar wajen karkatar da kudin, kamar yadda suka shaidawa Freedom Radio.
Freedom Radio ta tuntubi shugaban kasuwar Alhaji Ya’u Karas kan zargin, sai dai tsawon lokaci bai amsa kiran wayar da yake masa ba, da kuma gajeran sakon da ya aike masa.
Hakan ya sanya ta tuntubi mataimakin shugaban kasuwar Kurmin Alhaji Sani Sodangi wanda ya ce, tabbas gwamnati ta bada cek na miliyan 50 amma bai san a ina aka samu tsaiko ba.
Yan kasuwar sun bukaci gwamnati da ta samar da kwamitin da zai bibiyi inda tallafin nasu ya makale don fitar da su daga halin da suke ciki.
Rahoton: Bashir Ahmad Bahago
You must be logged in to post a comment Login