Labarai
Mutane 13 sun mutu sakamakon harin yan binding a Plateau

Akalla mutane 13 ne suka mutu a garuruwan Rachas da Rawuru da ke karamar hukumar Barkin Ladi, dake jihar Plateau , da Majiyoyin tsaro suka ce hare-haren sun faru ne da yammacin Talata, bayan kisan wasu matan Fulani biyu da wani yaro a kan hanyar Mangu
Shafin X, na Zagazola Makama, ya tabbatar da cewar harin na ramuwar gayya ne biyo bayan kisan mata da yaro ne wanda wasu ‘yan bindiga suka yi a baya.
Haka kuma kafar ta kara da cewa wadanda aka kashe suna cikin wata motar haya kusa da sansanin ‘yan hidimar kasa na NYSC lokacin da aka tare su, aka harbe su.
Sabon rikicin ya saka fargabar cewa rikicin Fulani da Berom na iya sake dawowa, kamar yadda ta faru a shekarar 2018, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Tuni dai aka yi jana’izar mutanen da aka kashe din a Rachas, inda shugaban karamar hukumar Barkin Ladi Stephen Gyang Pwajok, ya bayyana kashe-kashen a matsayin abun takaici da ba za a lamunta da su ba.
Haka kuma, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan tsaro na gaggawa tare da tattaunawa da shugabannin al’umma domin kawo karshen kisan gilla a yankin.
You must be logged in to post a comment Login