Labarai
Mutane 32 ne suka mutu a Turmutsutsun Anambra da Abuja- Yan sanda
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta ce, mutanen da suka rasa ransu a turmutsutsun da aka samu a jihar Anambra da birnin tarayya Abuja ya kai mutum 32.
Haka kuma rundunar ta ce mutum 22 ne suka mutu a turmutsutsun da ya faru a garin Okija na jihar Anambara, lokacin da wata gidauniya ke rabon tallafin kayan abincin bukukuwan Kirsimeti da suka haɗa da shinkafa da man girki ga masu ƙaramin ƙarfi a yankin.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu ƙananan yara 35 suka mutu a wani turmutsutsun a wajen wani biki a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Rundunar ‘yansan ƙasar ta kuma gargaɗi duka masu shirya rabon tallafin da su sanar da ita kafin aiwatar da rabon, domin kare aukuwar irin hakan a nan gaba.
Tuni dai shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu.
You must be logged in to post a comment Login