Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Mutane 44 sun mutu sakamakon harin ta’addanci a Burkina Faso

Published

on

Bayanai daga Burkina Faso na cewa fararen hula 44 ne suka mutu, a sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai kan kauyukan Kourakou da Tondobi da ke gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar, kamar yadda gwamnan yankin ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun kai hari kauyukan ne a tsakar daren ranar Juma’ar da ta gabata inda kuma suka bude wuta kan mai uwa da wabi lamarin da ya hallaka mutane 44.

Ta cikin Karin bayanin da ya yi, gwamnan lardin Rodolph Sorgho ya ce mutane 31 ne aka kashe a kauyen Kourakou sai wasu 13 da suka mutu a kauyen Todobi.

Rahotanni sun tabbatar da cewar Rabon da yankin ya ga irin wannan mummunan harin tun wanda aka kai a watan Yulin bara, wanda ya lakume da rayukan mutane 86.

Gwamna Rodolph ya ce tuni sojoji suka isa yankin don tabbatar da doka da oda da kuma kwantarwa da mutane hankali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!