Connect with us

Labarai

Mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewa da gobara a Qatar

Published

on

Mutane da dama sun jikkata bayan wata fashewa da gobara suka afku a yankin masana’antu na Ras Laffan da ke ƙasar Qatar a daren ranar Lahadi.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Qatar ta bayyana cewa fashewar ta samo asali ne daga wata matsalar fasaha da ta faru a cikin ɗaya daga cikin masana’antun yankin, lamarin da ya haddasa gobara.

 

A wata sanarwa da ta fitar daga baya, ma’aikatar ta tabbatar da cewa matsalar fasahar ta janyo raunuka ga wasu mutane, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda suka jikkata ko kuma tsananin raunukan da suka samu ba.

 

Kamfanin QatarEnergy ya ce fashewar ta faru ne yayin da ake ƙoƙarin dawo da ayyukan cibiyar samar da iskar gas ta Barzan da ke cikin Ras Laffan Industrial City, inda gobara ta tashi bayan fashewar.

 

Ras Laffan na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin samar da iskar gas mai ruwa (LNG) a duniya. Wurin ya taɓa fuskantar munanan hare-hare a lokacin rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda da Iran a gefe guda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!