Labarai
NCDC ta tabbatar mutuwar mutane 214 sakamakon zazzabin Lassa

Hukumar Kula da Yaduwar Cutuka ta kasa NCDC ta ce cutar zazzabin Lassa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 214 daga farkon shekarar da muke ciki ta 2026 zuwa yanzu.
Hukumar ta bayyana cewa adadin mace-macen ya karu zuwa kashi 25 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 18.9 cikin 100 da aka samu a shekarar 2025 data gabata.
A cewar NCDC, sabbin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a makonni 23 an samesu ne a jihohin Ondo, Edo, Bauchi da Ebonyi.
Rahoton ya nuna cewa cutar ta bazu zuwa jihohi 23 da kananan hukumomi 109 a fadin kasar nan.
Hukumar ta ce matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 su ne suka fi kamuwa da cutar.
You must be logged in to post a comment Login