Labarai
Mutane sama da dubu dari ne zasu iya samun aikin a sana’ar dogaro da kai a Kano duk shekara: Kungiya
- A kalla matasa dubu dari biyar ne za su samu aikin yi a kowacce shekara a Kano, matukar zasu mayar da hankali wajen sana’o’in dogaro da kai.
- Shugaban kungiyar Kungiyar rajin samar da kyakyawar tarbiyya da ci gaban matasa ta ce Malam Nura Ali Abdullahi Medille ne.
- Raina kananan sana’o’i da yin shaye-shaye tsakanin matasana, na daga ciki abubuwan da ke kara ta’azzara masu zaman banza.
- Ya kuma bayyana hakan da barazana ga matasa
Kungiyar rajin samar da kyakyawar tarbiyya da ci gaban matasa ta ce, a kalla matasa dubu dari biyar ne za su samu aikin yi a kowacce shekara a Kano, matukar zasu mayar da hankali wajen sana’o’in dogaro da kai.
Shugaban kungiyar Malam Nura Ali Abdullahi Medille ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da Freedom Radio a safiyar yau.
Tattaunawar dai ta mayar da hankali ne kan tushen gurbacewar tarbiyyar matasa da matsalolin da hakan ke haifarwa.
Ya kuma ce, ‘raina kananan sana’o’i da yin shaye-shaye tsakanin matasana, na daga ciki abubuwan da ke kawo koma baya wajan ci gaban matasa a wanna lokaci’.
Malam Nura Ali abdullahi Medille ya ce, ‘babbar barazanar gurbacewar tarbiyyar matasa bai wuce yadda za ta haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma’.
Rahoton: Aisha Aliyu Getso
You must be logged in to post a comment Login