Labarai
Mutanen gari sun ƙone waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane a Kano
Mutanen ƙauyen Rimi a ƙaramar hukumar Sumaila sun ƙone wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Wannan al’amari ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Juma’a.
Shaidun gani da ido sun ce, waɗanda ake zargin su uku ne, inda ɗaya daga cikin su ya miƙa kansa ga ofishin ƴan sanda.
Jama’ar garin a fusace sun yi ƙoƙarin ganin su hallaka shi, lamarin da yayi sanadiyar lalata wani sashe na ofishin ƴan sandan garin.
Rahotanni sun ce, ƴan sanda sun miƙa shi ga babban ofishin ƴan sanda na ƙaramar hukumar Sumaila.
Ƙarin bayani zai zo nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login