Connect with us

Labarai

Mutum Biyar sun mutu sakamakon harin ‘yan bindiga a jihar Kogi

Published

on

Akalla mutum biyar ne suka mutu bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai harin ramuwar gayya a ƙauyukan Abugi da Kuchinda da Mikugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja a Jihar Kogi.

 

Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne bayan kashe wani makiyayi da ake zargin wani ɗan ƙungiyar sintiri ta sa-kai ya yi bisa zargin satar shanu.

 

 

Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta umarci jami’an tsaro su kamo waɗanda suka kashe makiyayin da kuma waɗanda suka kai harin ramuwar gayya.

 

 

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya ba da umarnin a dawo da zaman lafiya cikin gaggawa tare da hukunta duk masu hannu a rikicin ba tare da la’akari da matsayinsu ko ƙabilarsu ba.

 

 

Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannu, tare da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen gudanar da bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!