Connect with us

Labarai

Immigration ta ce sabon tsarin buga Fasfo bai shafi rajista a jihohi ba

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta ce sabon tsarin da ta bullo da shi na buga fasfo a Abuja bai shafi yin rijista ko karɓar fasfo a jihohin ƙasar ba.

Hukumar ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa an cire cibiyoyin gudanar da fasfo daga Kano ba gaskiya ba ne, illa dai mutane sun yi kuskuren fahimtar sabon tsarin.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Kano, DSI Muhammad Auwal, ya ce sabon tsarin ya fara aiki tun farkon shekarar nan, inda aka fara aiwatar da shi a jihohi daban-daban.

Ya ce abin da aka mayar zuwa Abuja shi ne buga fasfo kawai, amma har yanzu ana ci gaba da yin rijista da kuma karɓar fasfo a dukkan cibiyoyin da ke jihohi, ciki har da nan Kano.

DSI Auwal ya kuma tabbatar da cewa takardar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ta fito ne daga hukumar, sai dai ya ce takarda ce ta cikin gida wadda ba a yi niyyar ta fito bainar jama’a ba.

A cewarsa, manufar mayar da buga fasfo wuri guda ita ce ƙarfafa tsaro, da rage yiwuwar buga fasfo na bogi.

Ya kuma ƙara da cewa jihar Legas tana cikin rukuni na gaba da za a aiwatar da sabon tsarin nan ba da jimawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!