Connect with us

Labarai

Jam’iyyar Accord ta bukaci shugaban EFCC ya yi murabus

Published

on

Jam’iyyar Accord ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa umarnin da ya bayar na cire takunkumin da aka sanya kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun. Sai dai jam’iyyar ta bukaci Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi murabus nan take, ko kuma Shugaba Tinubu ya sauke shi daga mukaminsa.

 

Shugaban Jam’iyyar Accord na ƙasa, Chief Maxwell Mgbudem, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja. Ya zargi EFCC da nuna son kai a siyasar Osun gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.

 

Jam’iyyar ta ce matakin daskarar da asusun gwamnatin Osun ya jefa EFCC cikin zargi da rashin adalci, tare da neman hukumomin tsaro da na zaɓe su kasance masu zaman kansu kuma su gudanar da aikinsu bisa doka.

 

Haka kuma, Accord ta yi kira ga INEC ta tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, sannan ta roƙi Shugaba Tinubu da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, su saki mambobin jam’iyyar 60 da ta ce har yanzu suna tsare.

 

A baya dai EFCC ta kare matakin daskarar da asusun gwamnatin Osun, tana mai cewa doka ta ba ta ikon yin hakan idan akwai zargin aikata laifukan kuɗi. Sai dai daga baya Shugaba Tinubu ya umarci hukumar ta koma kotu domin janye umarnin daskarar da asusun gwamnatin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!