Labarai
Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti
Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti
Da safiyar yau ne babban Kwamandan Hukumar yaki da safarar bil Adama ta kasa NAPTIP shiyyar Kano Shehu Umar ya sanar da cewar mutumin da ake zargi Malam Muhammadu Ojudi dake garin Rinji a karamar hukumar Madobi da laifin daure ‘ya ‘yan sa biyu da sarka da kuma sasari ya rasu a yau Juma’a a asibiti a dai-dai lokacin da ake shirin fara bincikar sa, kan laifin da ya aikata.
Sai dai gabanin rasuwar wanda ake zargi da aikata wannan lamari Muhammadu Ojudi ya bayyana dalilin sa na daukar wannan Mataki na daure yayan nasa biyu.
Amma dai kwamandan Hukumar shiyyar Kano Shehu Umar yace zasu cigaba da fadada bincike kan alamarin duk da rasuwar wanda ake zargi domin gano musabbabin daukar wannan mataki akan ‘ya’yan nasa.
Ana zargin Mutumin da ya daure ‘’yayansa biyu kan ‘yar taki zaman aure yayin da kuma dansa yake zargin cewar yana shaye shaye, a don haka ya dauki matakin ya sanya su a mari.
Mai haifin yaran yayi ikirarin cewar ‘ya’yan nasa na gagara kasancewar haka ya wajaba ya dauki matakin ya garkame su a cikin daki don su shiga taitayin su.
Malam Muhammad Ujudu ya rabo da mahaifiyar ‘ya’yan ne tun da jimawa, yayin da kuma yake zaune da kishiyar uwar su
Rahotanin sun bayyana cewar Mallam Muhammad Ujudu ya daure ‘yar tasa a wurin ne take Kashi da fitsari take kuma cin abinci kamar karya, yayin da ake miko mata ta taga.
Shi ma namijin ya shiga matsala irin wannnan ta daure shi da aka yi da sasari sannan sakamakon matsi da ya yi hakan yayi sanadiyyar rasuwar sa.