Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutuwar ƴar aiki a Kano: Ana mayarwa da ƴansanda martani

Published

on

Jama’a da dama na ci gaba da yin tsokaci kan rahoton rundunar ƴan sandan Kano game da rasa ran wata ƴar aiki.

Tun da farko an dai zargi wata mata da hallaka ƴar aikinta ta hanyar azabtarwa a unguwar Salanta Duka Wuya da ke Kano.

Sai dai ƴan sanda sun musanta zargin inda suka ce bincikensu ya gano cewa cizon Muzuru ne ya yi ajalin marigayiyar.

 

Me ya sanya jama’a ke shakku kan rahoton ƴan sanda?
A wata hira da Freedom Radio ta yi da yarinyar da ke aiki a gidan tare da marigayiyar ta bayyana cewa azabtarwa ce ta yi ajalin abokiyar aikinta.

Ta ce, matar gidan ta daki marigayiyar tare da caka mata ƙarfe a gabanta.

Waɗanda suka yiwa marigayiyar wankan gawa suma sun tabbatar da hakan inda suka ce sun ga tabbai kala-kala a jikinta.

Sannan sun ga ɗinki sabo a yayin da suke mata wankan gawar.

 

Ƴan sanda sun bada belin wadda ake zargin

Tun da farko ƴan sanda sun bayar da belin wadda ake zargin, sai dai daga baya sun ƙara cafke ta bayan karaɗi da Freedom Radio ta yi.

Haka ma, tun a farko wani ƙusa a rundunar ƴan sandan ya nemi Freedom Radio ta jingine labarin amma ba ta yi hakan ba.

Wani abin mamaki ma shi ne, yadda ƴan sanda suka riƙa bin diddigi tare da cafke waɗanda suka fara tsegumtawa Freedom Radio labarin.

 

Me ya faru a ƙarshe?
Ƴan sanda sun kamo ƴar aikin da ta bayyana yadda lamarin ya faru, tare da sake naɗarta cikin bidiyo kan ta ƙaryata abin da ta faɗa a baya.

 

Jama’a na yiwa ƴan sanda martani a kai
Bayan da jami’in hulɗa da jama’a ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Facebook jama’a sun yi ta tsokaci a kai kamar haka.

ZARGIN KISAN ‘YAR AIKI A UNGUWAR SALANTA SHARADA KANO

BINCIKE YAYI NISA, AN BANKA’DO ABUBUWA DA DAMA.

Posted by Abdullahi Haruna Kiyawa on Tuesday, February 2, 2021

 

Adama Muhammad Bala ta ce, “Amma maganar farko da yarinyar ta faɗa ya za ayi a ce ta yi ƙarya? Gaskiya dai insha Allah za ta fito”.

Auwal Magashi kuma ya ce, “Daga cizon muzuru yanzu kuma an koma shanye magani duka🤔🤔 ku na nufin over dose ta yi, ta mutu ke nan? Gaskiya Malam Kun raina ma na wayo.
Wato shi dai mara gata a ƙasar nan ya shiga uku, duk abin da ya faru da shi ba mai bi ma sa haƙƙin sa”.

Sai Muhammad Baballiya Zage ya ce, “Wallahi ku ji tsoron Allah a kan wannan lamari, kowa zai mutu kuma za ayi masa hisabi a kan dukkan rayuwar shi ta duniya.

To wallahi ku sani Allah ba zai bar wannan zalunci ya tafi haka ba”.

Jamilu Abdullahi Bau cewa ya yi, “Ya kamata hukumar ƴan sanda ta gayyato ƙaton muzurin da ake zargi da kuma magen da muzurun yake zuwa barbara gurinta su gurfana a gaba hukumar ƴansanda don ci gaban binciken, amma fa shawara nake bayarwa Allah ya taumaka amin”.

Shi kuwa Shamsuddeen Ɗalhatu Ɗan amana cewa ya yi, “Allah yasa mu gama da duniya lafiya amma wannan lamari akwai abin dubawa yarinyar tayi bayani sosai a freedom radio, Allah dai ya baku ikon adalci”.

Muhammad Sani Idris ya ce, “Abinda yarinyar nan take fada ƙarya ne, saboda abin da ta faɗa a Indaranka daban da abin da kuma yanzu aka shirya mata take faɗa daban”.

Har kawo yanzu dai jama’a na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a kai.

A gefe guda kuma hukumar kare haƙƙin ɗanadam ta ƙasa da ƙasa International Human Right Commission ta ce akwai alamar tambaya kan rahoton na ƴan sanda.

A don haka ma ta ce, tana ci gaba da tattara bayanai domin ɗaukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!