Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

COVID-19 : Ganduje ya gargadi Asibitioci masu zaman kan su

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci duk  masu cibiyoyin kiwon lafiya na zaman kansu, da su bi umarnin da kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar Corona ke bayar wa domin kare kansu da kuma marasa lafiya.

Gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau ya yin taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a dakin taro na Africa House.

Gwamna Ganduje ya ce a jiya an gano wani Asibiti mai zaman kansa yana karya ka’idoji na Covid 19 tare da shigar da marasa lafiyar da ke cikin mawuyacin hali ba tare da tura su zuwa ga kwamitin don killace masu cutar da kuma kulawa dasu ba.

A wani bangare kuma gwamnan jihar ya karbi bakuncin dattawan kasuwar Sabongari wadanda suka zo yiwa gwamnan godiya domin rage musu kudin haya a kasuwar saboda kalubalen cutar Covid 19 da ta shafi cigaban tattalin arzikin su da na kasa baki daya.

Wakiliya Zahrau Nasir ta ruwaito ya yin taron majalisar zartarwar gwamnan ya kuma karbi bakuncin shugabannin gudanarwar jami’ar Yusif maitama Sule karkashin jagorancin shugaban jami’ar Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa wanda ya yi karin haske kan nasarorin da aka samu a jami’ar kawo yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!