Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na gamsu da aikin jami’an tsaro a Katsina – Masari

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta nuna gamsuwar ta bisa aikin da jami’an soji da sauran jami’an tsaro ke yi wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai bai wa gwamnan jihar ta Kastina shawara kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina.

Sanarwar ta ce, shakka babu hadakar jami’an tsaro dake tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma a jihar suna iya kokarinsu wajen ganin lamura sun kyautata.

Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, akwai bukatar jami’an soji su ci gaba da yin rangadi a yankunan da rashin tsaro yayi kamari don dakile duk wani yunkuri na ‘yan ta’adda.

Sanarwar ta kuma godewa kafafen yada labarai wajen wayar da kan al’umma, game da matsalar tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!