Addini
Na kadu matuka da ganin sunayen mutanen da ke daukar nauyin Boko Haram – BUHARI
Fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin tarayya ta gano masu daukar nauyin ‘yan ta’addar Boko haram da ‘yan bindiga da ke ta kashe-kashen jama’a, babu gaira babu dalili a sassa daban-daban na kasar nan.
A cewar fadar shugaban kasa bankado wadanda ke da hannu cikin lamarin ya yi matukar kadata.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a daren jiya talata.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labaran ya bayyana hakan ne ya yin zantawa da gidan talabijin na Channels, ya na mai cewa, ba za a saurarawa kowa ba komai girman mutum ko da kuwa dan siyasa ne matukar aka gano da hannunsa cikin lamarin za ayi mishi hukunci daidai da laifin da ya aikata.
Ya ce bincike ya gano cewa cikin masu daukar nauyin ‘yan boko haram da ‘yan bindiga akwai masu sana’ar canjin kudaden ketare wadanda suke da alaka da wasu gungun masu aikata laifuka na kasa da kasa da ke kasashen waje.
Malam Garba Shehu ya kuma ce gaskiya ne zargin da ake yi cewa akwai alaka tsakanin ‘yan boko haram da ‘yan bindiga da ke aikata ta’asa a wasu yankuna na kasar nan saboda akwai kwararan hujjoji da ya tabbatar da hakan.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labaran ya kuma ce sun samu hujjoji da ke nuna cewa ana turo da makudan kudade ga kungiyar boko haram daga kasar hadaddiyar daular larabawa.
‘‘Tuni jami’an tsaro sun kama mutane da dama wadanda ake zargin suna da hannu cikin badakalar kuma ana ci gaba da bincike da zaran komai ya kammala za a bayyana sunayen su ga al’ummar kasa’’ a cewar Malam Garba Shehu.
You must be logged in to post a comment Login