Labarai
Na kwato Naira biliyan 309 na NNPC – Magu
Dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, ya ce, ya kwato akalla naira biliyan dari uku da ashirin da tara daga wajen dillalan man fetur masu taurin bashi, inda ya sanya kudaden a asusun kamfanin mai na kasa NNPC.
Hakan na cikin wata wasika ce na kariya da dakataccen shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya rubutawa kwamitin shugaban kasa da ke gudanar da binciken shugabancin da yayi a EFCC karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara, mai shari’a Ayo Salami.
A cikin wata sanarwa da lauyansa Wahab Shittu ya fitar, ya ce, batun kudaden kamfanin na NNPC bai taso ba a lokacin da ake yi masa tambayoyi, saboda ya ce yamadidin da ake yi kan batun ne suka mika da takaddu na hujjjoji da ta nuna hukumar ta EFCC ta sanya kudaden a asusun kamfanin na NNPC.
Haka zalika ya ce wannan kokari da hukumar ta EFCC ta yi shi ya sanya ma kamfanin da ke kula da farashin man fetir PPRA ya rubuta wasika mai dauke da kwanan wata goma sha bakwai ga watan Agusta a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai tare da godewa hukumar ta EFCC .
You must be logged in to post a comment Login