Labarai
Na yi dana sanin yin aiki da gwamnatin Buhari – Solomon Dalung
Tsohon ministan matasa da harkokin wasannin kasar Solomon Dalung ya ce yayi da ya sanin aiki da gwamnatin shugaba Buhari.
Dalung ya sanar da hakan a wata hira ta musamman da Freedom Radio.
Ya ce, gwamnatin da suka gada sun tarar da abubuwa masu inganci musamman ma a harkar tsaro.
“A yanzu matsalar tsaro ta sanya al’umma da dama a yankin Arewa sun bar muhallansu, wasun suna kwana a dazuka”.
Solomon Dalung ya kuma zargi yadda gwamnati mai ci a yanzu ke wadaƙa da kuɗaɗen al’umma da sunan samar da ayyukan ci gaba.
“A baya majalisun ƙasar nan ba sa gaggawar amincewa da duk wani kasafin kuɗi da aka kai musu, amma a yanzu da zarar an gabatar musu da kasafi suke amincewa da shi”.
Dalung ya kuma ce, ayyuka da dama da gwamnatin baya ta gada ta gaza ƙarasa su, duk daaƙudan kuɗaɗen da ake fitarwa domin kammala su.
Tsohon ministan ya kuma ce ita kanta jam’iyyar APC ɗin na tafiya ne bisa umarnin wasu tsirarun mutane waɗanda basu da kishin ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login