Connect with us

Labarai

Na yi dana sanin yin aiki da gwamnatin Buhari – Solomon Dalung

Published

on

Tsohon ministan matasa da harkokin wasannin kasar Solomon Dalung ya ce yayi da ya sanin aiki da gwamnatin shugaba Buhari.

Dalung ya sanar da hakan a wata hira ta musamman da Freedom Radio.

Ya ce, gwamnatin da suka gada sun tarar da abubuwa masu inganci musamman ma a harkar tsaro.

A yanzu matsalar tsaro ta sanya al’umma da dama a yankin Arewa sun bar muhallansu, wasun suna kwana a dazuka”.

Solomon Dalung ya kuma zargi yadda gwamnati mai ci a yanzu ke wadaƙa da kuɗaɗen al’umma da sunan samar da ayyukan ci gaba.

“A baya majalisun ƙasar nan ba sa gaggawar amincewa da duk wani kasafin kuɗi da aka kai musu, amma a yanzu da zarar an gabatar musu da kasafi suke amincewa da shi”.

Dalung ya kuma ce, ayyuka da dama da gwamnatin baya ta gada ta gaza ƙarasa su, duk daaƙudan kuɗaɗen da ake fitarwa domin kammala su.

Tsohon ministan ya kuma ce ita kanta jam’iyyar APC ɗin na tafiya ne bisa umarnin wasu tsirarun mutane waɗanda basu da kishin ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!