Kasuwanci
NACCIMA ta yi na’am da sabuwar dokar hada-hadar man fetur a Najeriya

Cibiyar Habaka Kasuwanci Masana’antu Ma’adanai da Noma ta Najeriya (NACCIMA) ta yi na’am da sabuwar dokar hada-hadar man fetur (PIB) a kasar nan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ya sahale tare da sanya hannu a dokar.
Cibiyar ta kuma bayyana dokar a matsayin wani yunkuri na sauya salon bangaren hada-hadar man fetur da iskar gas don bawa masu sanya hannu jari na gida da na waje kwarin gwiwa.
You must be logged in to post a comment Login