Labarai
Mutuwar Mutane: NAFDAC ta kama wadanda ake zargi da sayar da jabun sinadaren lemo a Kano
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, ta tabbatar da kama mutanen da ake zargi da sayar da sinadaren kara dandanon lemon da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a Jihar Kano.
Shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar Sayo Akintola ya fitar.
Mista Akintola ya ce tuni suka mikawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje rahoton binciken da suka gudanar, bayan sun gano cewa sinadaren ne suka hallaka mutane uku a Kano.
“A cikin sinadarai biyar da muka gudanar da bincike a kansu, biyu ne kadai suke da rajistar NAFDAC, yayin da uku kuma ba su da ita,” a cewar Akintola.
Hukumar ta gargadi jama’a da su kaucewa amfani da duk wani sinadari mai kara dandanon lemo ko ma abinci, sakamakon illar da yake haifarwa ga lafiyar bil’adama.
You must be logged in to post a comment Login