Labarai
NAHCON: ta yi jigilar maniyatan aikin hajji dubu sittin da biyar a bana
Kimanin ‘yan Najeriya maniyata aikin hajjin bana dubu sittin dabiyar ne hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON tayi jigilar su zuwa kasar mai tsariki.
Wani babban jami’I a hukumar ta NAHCON Dr, Aliyu Tanko ne ya shedawa manema labarai a birnin Makkah cewa tuni hukumar ta kammala shirye-shirye don saukakawa maniyata aikin hajji don sauke farali wanda za’a fara a ranar Asabar mai zuwa.
Dr, Aliyu ya ce hukumar ta kammala jigilar dukkannin ‘yan Najeriya zuwa kasa mai tsarki kuma tuni suka fara yin ziyara wurare masu daraja.
Haka zalika ya yabawa hukumomin kasar Saudiya saboda hadin kan da suke baiwa hukumar ta NAHCON wajen ganin ‘yan Najeriya sun sami sauki a yayin yin jifan shedan