Labarai
NAHCON za ta fara yi wa maniyyata binciken lafiya
Hukumar jin daɗin alhazai ta birnin Tarayyar Abuja, ta bayyana ranakun 5 zuwa 7 ga watan Mayu a matsayin ranar da za ta fara gudanar da bincike lafiya ga maniyyatan bana.
Daraktan hukumar Malam Abubakar Evuti, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar Malam Muhammad Aliyu ya fitar a Talatar nan.
Shugaban ya ce, za a fara yi wa maniyyata aikin hajjin bana allurar riga-kafin daga 15 ga watan na Mayu zuwa 17 ga watan, saboda a samu kammala shirye-shiryen maniyyatan da wuri.
Haka kuma, ya shawarci maniyyata da su tabbatar sun yi duk abubuwan da hukumar ta gindaya domin ba su damar gudanar da aikin hajjin yadda ya kamata.
Malam Abubakar Evuti, ya ja kunnen waɗanda har yanzu ba su mayar da fom dinsu ba da su hanzarta yin hakan ta hanyar kai fasfo ɗinsu.
You must be logged in to post a comment Login