Labaran Kano
Naira miliyan dari hudu da hamsin da daya akai amfani da su wajen siyan Awaki a Kano : Waiya
Gwamnatin jihar Kano ta ce Naira miliyan dari hudu da hamsin da daya ne akai amfani da su wajen siyan Akuyoyi dubu bakwai da dari da hamsin da takwai, akasin yadda wasu ke yadawa cewar an sayi awakina na sama da naira biliyan biyu.
Kwamishinanan ma’aikatar yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radiyo kan batun siyan awakin da gwamnati ta yi.
A ranar 20 ga watan Janairun 2025 ne dai gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon tallafin awaki da raguna da shanu ga manoma.
Ya kuma ce maganar da ake cewa kowacce akuya ta tashi a kan naira dubu dari uku da hamsin ba gaskiya bane
An kuma sai raguna guda 1,975 inda za a rabawa mutane 987 da kudaden su ya kai naira miliyan dari uku da miliyan hamsin da daya da dubu dari bakwai da hamsin.
Ya kuma ce an sai Shanu guda 1400 wanda za a rabawa mutane 700 da kudin su ya kai Naira, Biliyan daya da miliyan dari da Ashirin.
Waiya ya kuma ce an ware naira miliyan dari hudu da ashirin da bakwai da dubu dari tara da hamsin da Takwas.
A cewar sa idan aka tara kudin shine zai tasamma naira biliyan biyu da miliyan dari uku
You must be logged in to post a comment Login