Labarai
Najeriya da EU za su yi taron Kasuwanci karo na 10

Kungiyar tarayyar Turai da Gwamnatin Tarayyar Najeriya sun sanar da gudanar da Taron Kasuwanci tsakanin Najeriya da Tarayyar Turai karo na 10 a Legas ranar 25 ga Yunin 2026. Taron ya zama muhimmiyar kafa ta ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu, tare da mai da hankali kan sauya tattaunawa zuwa ainihin haɗin gwiwar kasuwanci da zuba jari.
A bana, taron zai mayar da hankali kan samar da jarin masu zaman kansu, ƙarfafa sarkokin samar da kayayyaki da ayyuka, da kuma faɗaɗa damar kasuwanci ga kamfanonin Najeriya da na Turai. Haka kuma za a gudanar da tattaunawa tsakanin jami’an gwamnati da shugabannin kamfanoni, ganawa tsakanin ‘yan kasuwa da masu zuba jari, da kuma baje kolin damar zuba jari.
Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Gautier Mignot, ya ce taron na nuna ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu. Shi ma Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama ta jawo zuba jari da tallafawa ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login