Labarai
Gwamnatin Zamfara ta gargadi ma’aikatan lafiya da ke ƙin zuwa aiki

Gwamnatin Jihar Zamfara ta gargadi ma’aikatan lafiya kan rashin zuwa aiki tare da yin barazanar ɗaukar matakan ladabtarwa ga duk wanda aka samu da sakaci a wurin aikinsa.
Kwamishinar Lafiya ta jihar, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, ce ta bayyana hakan ga manema labarai.
Gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga ingantaccen aikin kiwon lafiya ba.
Ta bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba cibiyoyin lafiya a sassan jihar, inda ta jaddada aniyar gwamnati na inganta ayyukan kiwon lafiya da samar da ingantattun ayyuka ga al’umma.
A yayin ziyarar, kwamishinar ta nuna rashin gamsuwa da yanayin tsaftar Babban Asibitin Gusau, tare da umartar kamfanin da ke kula da tsaftar wajen ya gyara aikinsa cikin gaggawa.
Dakta Nafisa Muhammad Maradun ta kuma gargadi masu gudanar da asibitoci masu zaman kansu da su bi ƙa’idojin kiwon lafiya, tana mai cewa duk cibiyar da aka samu tana aiki ƙasa da ƙa’idar da aka tanada za a iya rufe ta.
You must be logged in to post a comment Login