Labarai
Yan sandan sun cafke mutane 4 tare da kashe wasu biyu bisa zarginsu da hannu a sace kanwar tsohon Adelabu

Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta tabbatar da cafke mutane hudu tare da kashe wasu biyu a yankin Ayegun da ke karamar hukumar Oluyole a Ibadan, da ake zargi da hannu a sace kanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, mai suna Busola, tare da ’ya’yanta biyu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Oluwagbemiga Abimbola, ya ce jami’ansu sun samu bayanan sirri ne wanda ya kai su maboyar masu garkuwar, inda suka ceto wadanda aka sace bayan shafe sa’o’i suna gudanar da aiki.
Ya kara da cewa an kwato makamai daban-daban ciki har da bindigar pump-action a wurin.
An sace Busola da tagwayen ’ya’yanta masu shekaru 12 a safiyar Laraba a yankin Elewura-Challenge na Ibadan a makon da ya gabata.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake cigaba da kiraye-kirayen ceato dalibai da malamai da aka sace a jihar ta Oyo a baya bayan nan.
You must be logged in to post a comment Login