Labarai
Najeriya da majalisar dinkin duniya da Tarayyar Turai za su tallafawa marasa galihu – Buhari
Ma’aikatar lura da harkokin mata ta kasa da hadin gwiwa da hukumar dakile cuta mai karya garkuwar jiki da majalissar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyar turai sun kaddamar da shirin bada tallafi ga mata marasa galihu don rage radadin halin da aka shiga a sanadiyar annobar Corona.
Da yake kaddamar da shirin bada tallafin Darakata Janar na hukumar dakile cuta mai karya garkuwar jiki Dakata Gambo Aliyu, yace annobar Corona ta taba ko wanne bangare na rayuwar al’umma ciki kuwa har da tattalin arzikin kasa.
Da ta ke jawabi yayin kaddamar da bada tallafin Ministar ma’aikatar lura da harkokin mata Pauline Tallen, ta ce yanzu haka suna gudanar da aiki da dukkanin masu ruwa da tsaki don ganin an tallafawa wasu jihohi 15 da annobar Corona ta fi yiwa ta’annati a kasar nan ciki har da nan Kano.
Abubuwan da aka raba kuwa sun hadar da kudi da takunkumin rufe hanci da sabulu da kuma sinadarin wanke hannu wato sanitizer, inda mata da matasa dubu 18 suka amfana.
You must be logged in to post a comment Login