Kiwon Lafiya
Najeriya da wasu kasashe duniya zasu fuskanci kusufin wata
Hukumar binciken sararin samaniya ta kasa tace Najeriya da sauran kasashen duniya zasu fuskanci kusufin wata ranar ashirin da daya ga watan Janairun da muke ciki.
Wannan na kunshe a wata sanarwa da shugaban sashen yada labaran hukumar Dakta Felix Alle ya fitar yau a Abuja.
A cewar sa kusufin wata alama ce da ke nuna rashin lafiyar wata, inda ya ke nuna alamar duhu a jikin sa da zarar ya bayyana a sararin samaniya.
Ya bayyana cewa rashin lafiyar watan na faruwa ne sakamakon kaucewa hanyar da ya saba bi da ake samu.
Yace watan zai fara kusufin ne da misalin karfe hudu da minti talatin da uku na asuba, ana kuma sa ran samun saukin sa da misalin karfe shida da minti arba’in da uku na safiyar ranar Litinin mai zuwa.
Dakta Felix ya kuma bayyana cewa ana sa ran yankunan Arewa, Kudu da kuma yammacin kasar Amurka, sai kuma sauran kasashen Turai da yankin Asiya hadi da kasashen Yammacin Afirka ne zasu fuskancin kusufin watan a ranar Litinin.