Labaran Wasanni
Najeriya ka iya rasa tikitin Kofin Duniya na Rubgy – Martin Crawford
Shugaban hukumar ƙwallon Zari Ruga ta (Rugby ) na jihar Kano, Mista Martin Crawford, ya ce, Najeriya na fuskantar Barazanar kasa halartar gasar Kofin Duniya na Rugby , sakamakon rushe shugabannin hukumomin wasanni daban-daban na Najeriya, da Ministan wasa Sunday Dare yayi.
Crawford, ya bayyana a zantawar sa da ƴan Jarida a harabar ofishin hukumar ranar Talata 04 Mayu 2021 cewa.
“Ina tabbatar muku da cewar hukuncin Ministan ya karya dukkan ƙa’idojin hukumar Olympic da ta Rubgy ta Duniya na hana Gwamnati yin Katsalandan a harkokin wasanni”.
“Mun Kashe ma’udan kuɗi, kana ƴan wasa sun kashe nasu kuɗaɗen daga Amurka, Ingila Italiya duk sun amince da zuwa buga wasannin share fagen shiga gasar, tare da ƙwararrun ƴan wasan mu na Kano da Legas, amma sai gashi ana neman watsa lamarin, wannan ba abu ne mai daɗi ba” inji Crawford .
Da yake nasa jawabin, Ɗan Kwamitin zartarwa na hukumar kwallon Rubgy ta kasa (NRFF), David Emeana, ya buƙaci Ministan da ya janye hukuncin da ya ɗauka, don ci gaba da shirye-shiryen tunkarar gasar.
A cewar sa, rashin yin hakan zai jawo wa Najeriya kora ko dakatarwa daga hukumar ƙwallon Rubgy ta Duniya, na tsawon shekaru huɗu kamar yadda aka taɓa fuskanta a shekarun baya.
Najeriya, na shirye-shiryen tunkarar takwarorinta na Afirka a wasannin share fagen shiga gasar Kofin Duniya, da za gudanar a Ouagadougou babban Birnin kasar Burkina Faso, da tawagar ta zata kammala shiri zuwa ranar 24 ga Mayu.
You must be logged in to post a comment Login