Labarai
Najeriya na bukatar kasar Saudiya ta sa hannu wajen bunkasa harkokin mai
Kasar Saudi Arebiya na shirye-shiryen gina matatar mai a kasar nan.
Ministan makamashi da albarkatun kasa na kasar ta Saudi arebiya, Khalid Al Falih ne ya bayyana haka, yayin ganawa da karamin ministan man fetur na kasar nan, Ibe Kachikwu, a Riyadh babban birnin kasar ta Saudiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar albarkatun man fetur ta kasar nan, ta fitar, jiya a Abuja.
Sanarwar ta ruwaito karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu na cewa, ganin yadda kasar ta Saudi arebiya ta yi nisa wajen fasaha a bangaren man fetur, hakan ne ya sa kasar nan ta ke bukatar Saudiyan ta sa hannu wajen bunkasa harkokin mai a Najeriya.
Ta cikin sanarwar dai, Ibe Kachikwu, ya kuma ce, a shekarar da ta gabata, kamfanin mai na kasar Saudi arebiya ‘Aramco’ kwatankwacin kamfanin mai na kasa (NNPC) ya samu ribar dala biliyan dari biyu