Labarai
Najeriya ta yi asarar sama da Biliyan 940 na fitar da kayayyaki zuwa Amurka- NBS

Hukumar kiddiga ta kasa NBS ta ce kasar nan tayi asarar kusan sama da Naira Biliyan 940 na fitar da kayayyaki zuwa Amurka a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 bayan Karin harajin da Shugaban Amurka Donal Trump yayi
Bayanin na NBS sun bayyana cewa daga Watan Junairun zuwa Satumba na wannan shekara kasar nan ta fitar da kayayyaki da kimarsa ta kai Tiriliyan 3.65 zuwa Amurka Wanda yayi Kasa da naira Tiriliyan 4.59 da aka fitar adaidai wannan lokaci a 2024 da hakan na nufin ansamu raguwar Kashi 20.5
NBS ta ce wannan bayanin ya zo ne a dai dai lokacin da gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da Sabon tsarin harajin inda Shugaban Amurka ya kara harajin kasar nan daga Kashi 14 zuwa Kashi 15 cikin dari
Harajin dai ya fara aiki ne a ranar 7 ga Agustan 2025 Wanda ya shafi kayayyakin da bana mai ba a ake fitarwa.
You must be logged in to post a comment Login