Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya za ta fara buga wa ƙasar Gambia kuɗi – Emefiele

Published

on

Babban bankin ƙasa (CBN) ya amince Najeriya ta fara buga kuɗi ga ƙasar Gambia.

 

Kudin Gambia dai ana kiranshi da suna ‘Dalasi’.

 

Gwamnan bankin na CBN Godwin Emefiele shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau a Abuja.

 

Ya ce, ya tattauna da gwamnan babban bankin ƙasar Gambia Mista Buah Saidy wanda ya kawo masa ziyara ofishinsa da ke Abuja a yau talata.

 

A nasa ɓangaren kamfanin buga kuɗi da muhimman takardun gwamnati na ƙasa, ya ce, a shirye yake ya aiwatar da wannan umarni da bankin na CBN ya yi yarjejeniya da ƙasar ta Zambia.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!