Kiwon Lafiya
Najeriya za ta karbi tallafin dala milyan 143 daga asusun tallafawa lafiya – Global Fund
Najeriya za ta karbi jimillar kudi kimanin dala miliyan 143 daga asusun duniya na tallafawa harkokin lafiya wato ‘Global Fund’ don ci gaba da yaki da cutar tarin fuka.
A cewar asusun zai bai wa Najeriya kudaden ne cikin wa’adin shekaru uku masu zuwa.
Babban jami’in da ke kula da cututtuka a asusun Eliud Wanerdwalo ne ya bayyana hakan, yayin taron yaki da cutar tarin fuka karo na 33 da aka gudanar ta kafar internet.
Taron dai ya samu halartar ministocin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki daga wasu kasashen afirka guda goma sha daya.
Ya ce jimillar kudaden da asusun zai tallafawa kasashen baki daya cikin shekaru uku masu zuwa ya kai dala miliyan dari biyar, inda Najeriya ita kadai za ta samu dala miliyan dari da arba’in da uku.
You must be logged in to post a comment Login