Labarai
Bikin ranar yara: An kaiwa marayu tallafin abinci don taya su murna
Kungiyar ma’aikatan asusun kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF anan Kano, ta bukaci a rika taimakawa marayu don rage musu radadin rashin iyaye da suke fama da shi.
Shugaban kungiyar Saka Ibrahim Adebayo ne yayi wannan kiran, lokacin da kungiyar ta kai wa gidan marayu da ke unguwar Nassarawa a nan Kano kayayyakin abinci.
Saka Ibrahim Adebayo ya ce kungiyar ta ziyarci gidan marayun ne a wani bangare na bikin ranar yara ta duniya da aka gudanar a ranar 20 ga watan Nuwamba, don taya su murnar bikin ranar.
Da ta ke mai da jawabi, jami’ar da ke kula da gidan marayun na unguwar Nassarawa, Hajiya Aisha Sani Kurawa, ta godewa kungiyar tare da fatan wasu kungiyoyin za su yi koyi da su.
Wakilinmu Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, kayayyakin da kungiyar ta tallafawa gidan yara marayun da ke Nassarawa sun hada da: Shinkafa, wake, sabulan wanki da na wanka da man girki da sauran wasu kayayyakin da dama.
You must be logged in to post a comment Login