Labarai
Najeriya zata zarce China yawan jama’a a nan gaba – Bincike
Wani sakamakon bincike da jami’ar Washington da ke kasar Amurka ta fitar ya nuna cewa nan da shekaru tamanin masu zuwa adadin al’ummar Najeriya zasu zarce na kasar China yawa.
Kasar China dai a yanzu ita ce kasa mafi yawan al’umma a duniya, wanda bayanai suka ce nan da shekaru hudu masu zuwa, adadin jama’ar kasar ka iya kaiwa sama da biliyan daya da miliyan dari hudu.
Sai dai binciken da masana a jami’ar ta Washington, ya nuna cewa, nan da shekarar dubu biyu da dari daya adadin al’ummar kasar ta China zai yi matukar raguwa zuwa miliyan dari bakwai da talatin da biyu, lamarin da zai sa kasar Indiya ta zama kasa mafi yawan jama’a a duniya.
Jagoran masu binciken a jami’ar ta Washington, farfesa Christopher Murray, ya ce, nan da shekaru tamanin masu zuwa al’ummar Najeriya za su kai miliyan dari bakwai da casa’in da daya.
You must be logged in to post a comment Login