Labarai
Nan bada jimawa za’a fara fitar da shinkafa zuwa ketare -Nanono
Ministan aikin gona da raya karkara Alhaji Sabo Nanono ya ce nan ba da dadewa ba, kasar nan za ta fara fitar da shinkafa zuwa ketare sakamakon bunkasar noman shinkafar da ake samu a baya-bayan nan.
Ministan ya bayyana hakan ne jiya a garin Kura da ke nan jihar Kano, yayin da ya ke duba masana’antun sarrafa shinkafa.
Y ace an samu bunkasar noma da sarrafa shinkafa a kasar nan tun bayan da gwamnati ta rufe kan iyakokin kasar nan na kan tudu.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito Alhaji Sabo Nanono wanda ya samu rakiyar ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad na cewa, ya gamsu matuka da yadda harkokin sarrafa shinkafa ke gudana.
Zamu samar da doka kan fitar da fatu kasashen waje-Nanono
Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono
Wani Sabon gidan abincin Naira Talatin ya hana wasu Almajirai bara a Kano.
Za’a fadada gidan abincin N30 zuwa kananan hukumomi 44 na Kano
A cewar minista aikin gonan, garin Kura ya jima yana bada gudunmawa wajen samar da kayayyakin amfanin gona wadanda suka hada da: Tumatur da Shinkafa da kuma Masara.
Da yake jawabi, ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad, ya ce, gwamnatin tarayya a shirye take wajen ci gaba da tallafawa masu ruwa da tsaki ta bangaren noma da sarrafa shinkafa