Labaran Kano
Za’a fadada gidan abincin N30 zuwa kananan hukumomi 44 na Kano
Wani dan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Abdussalam Salisu Bacha ya kai ziyara sabon gidan cin abinci N30 a unguwar Sani Mainagge dake nan Kano.
Dan kasuwar ya bada tallafin kudi har naira dubu ashirin ga mai gidan abincin bisa kokarinsa na aiwatar da abinda ministan noma yayi ikrari.
Sannan yayi alkawarin zai isar da wannan sakon ga ministan Noma na kasa Alhaji Sabo Nanono.
Wakiliyarmu Umma Sulaiman Sagagi ta rawaito mana cewa mai gidan abincin Alhaji Haruna Kassim da mai dakinsa Hajiya Sadiya Haruna sun nuna farin cikin su da wannan gudummuwa da aka basu, sannan tuni suka fara yunkurin fadada wannan gidan abinci zuwa kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin samarwa matasa aikin yi.
Idan zaku iya tunawa dai an bude wannan gidan abinci ne biyo bayan furucin da ministan Noma Alhaji Sabo Nanono yayi na cewar mutum zai iya cin abinci ya batse akan naira 30 kacal.
Gidan abincin ya fara ne da jarin N2,500 inda suka fara sayar da wasa-wasa wato hadin garin kwaki, sai dai izuwa yanzu jarinsu ya kai ha N8,000 da kuma ma’aikata har guda hudu.
RUBUTU MAI ALAKA:
Ya zama wajibi al’umma su baiwa ilimi fifiko-Dr Bashir Sani
Za’a karrama Zakin da ya kufce daga gidan Zoo