Kasuwanci
NBS: Zuwa watan Disambar 2020 kawai ana bin Najeriya bashin naira tiriliyan 32
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce basukan da ake bin jihohi da gwamnatin tarayya ya zuwa watan Disamba ya kai naira tiriliyan talatin da biyu da biliyan casa’in da biyu.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da hukumar ta NBS ta wallafa a shafinta na internet.
Sanarwar ta ce tiriliyan goma sha biyu da biliyan saba’in da daya basuka ne da aka ciyo su daga ketare, yayin da tiriliyan ashirin da biliyan ashirin da daya basuka ne na cikin gida.
Rahoton ya kuma ce dala biliyan goma sha bakwai da miliyan casa’in da uku basuka ne da aka ciyo su daga bankin Exim na China da JICA da India da KFW, yayin da dala biliyan goma sha daya da miliyan goma sha bakwai aka karbo su daga bankunan kasuwanci na turai da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login