Labarai
NCDC ta yi gargadin barkewar annobar Yellow Fever
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC, ta ce akwai yiwuwar karuwar cutar zazzabin Yellow Fever a wasu jihohin kasar nan.
Shugaban sashen yada labarai da lura da aiyyukan gaggawa na cibiyar Dakta Yahaya Disu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Dakta Yahaya Disu, ya ce sakamamon rashin daukar matakan gaggawa na dakile cutar ya sanya aka samu karuwar masu cutar a wasu jihohin Najeriya.
Har ma yace, a yanzu haka cibiyar na kokarin samar da cibiyoyin yin rigakafi a fadin kasar nan tare da hadin gwiwar jihohi.
A baya bayan nan dai an samu rahotannin barkewar cutar, a jihohin Bauchi da Ondo da Delta, sai jihar Enugu da lamarin ya yi kamari har cutar tayi sanadiyyar mutuwar mutumane 57.
You must be logged in to post a comment Login