Labarai
NDLEA ta bankado masu hada maganin Akuskura
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta bankado wani waje a jihar Adamawa da ake hada maganin Akuskura da ya ke jefa mutane cikin halin maye.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi a Abuja.
Ya ce a lokacin da aka kai farmakin, jami’an hukumar ta NDLEA sun tarar da ana ci gaba da gudanar da ayyukan hada kayan saka mayen na akuskura.
Haka kuma, ya kara da cewa, an gano wurin ne inda ake hada maganin tare da aike wa da shi kasashen Chadi da Kamaru da kumaJamhuriyar Nijar.
You must be logged in to post a comment Login