Labarai
NDLEA ta cafke Makafi uku da ke safarar kwayoyi
Hukumar yaki da sha da fatucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta sanar da kama wasu Makafi uku da ta ke zargin su da aikata safarar kwayoyi daga jihar Lagos zuwa Kano.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa jami’an hukumar sun kama mutanen ne bayan bayanan sirri da daya daga cikin su mai suna Adamu Hassan ya bawa jami’an hukumar bayan an kama shi.
Babafemi ya kuma ce, sun kama Adamu Hassan ne a ranar 28 ga watan Oktoban da ya gabata dauke da kwaya mai nauyin kilogiram 12 a hannun sa akan titin Gwagwalada da ke cikin babban birnin tarayya Abuja yayin da yake kan hanyarsa daga Lagos zuwa Kano.
Jami’in ya kara da cewa bincike ya tabbatar da cewa wanda aka kama din bai san me ke cikin jakar da aka mika masa ya kai zuwa Kano ba.
Babafemi ya kuma ce, hakan ce ta sa suka kai samame da aka kama shugaban kungiyarsu Bello Abubakar, mai shekaru 45, shi ma mai nakasa ta idanu.
You must be logged in to post a comment Login