Labarai
NDLEA ta cafke yar Afirka ta Kudu dauke da hodar Iblis a filin jirgi na Abuja

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama wata ’yar ƙasar Afirka ta Kudu mai shekara 38 Will Jessica Ann a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan gano kilo 5.75 na hodar Iblis da aka ɓoye a cikin kayanta.
Hukumar ta ce, matar ta yi ƙoƙarin amfani da ɗanta mai shekara uku a matsayin kariya don kauce wa cikakken binciken jami’an tsaro.
An kama ta ne bayan isowarta daga birnin Doha na ƙasar Qatar.
NDLEA ta bayyana cewa da farko matar ta musanta mallakar jakunkunan da aka kama da hodar, amma bincike ya nuna alamun kayanta sun yi daidai da bayanan da ke Fasfo ɗinta.
Wannan dai na zuwa ne yayin da kasar Afrika ta Kudun ke cikin yanayin zanga-zangar kin bakin haure wadda ta yi sanadiyyar taso keyar daruruwan yan Najeriya daga kasar.
You must be logged in to post a comment Login