Labarai
Yan sanda na shirin gurfanar da Adeniyi bisa zargin da bayyana kansa a matsayin shugaban PFIPC

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukumar bogi ta PFIPC, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a gobe Talata.
Ana tuhumarsa tare da wasu mutum biyu kan laifuka takwas da suka hada da ƙirƙirar takardun bogi.
A cewar takardun kotu, daga cikin shaidun da gwamnati za ta gabatar akwai Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu jami’an gwamnati da na ‘yan sanda. Haka kuma, ana shirin gabatar da wasu takardu da suka hada da wasikar nadin aiki ta bogi, rahoton binciken ‘yan sanda da kuma wasu takardun da ake zargin Adeyemi ya yi amfani da su wajen neman amincewa da bude asusu da gudanar da ayyukan hukumar.
A baya, dain Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da kammala shi cikin kwanaki 30.
You must be logged in to post a comment Login