Labarai
NDLEA ta kara tsaurara matakan tsaro a wannan lokaci na bukukuwan sallah a Kano.
- Shugaban hukumar NDLEA a Kano ya ce yawanci laifukan ta’addanci ana yinsu ne bayan shaye-shaye.
- Yayi kira ga matasa da su guji shaye-shayen don gujewa abinda kaje ya dawo.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce, ‘ta kara tsaurara matakan tsaro a wannan lokaci na bukukuwan sallah, domin kama dilolin da ke sayar da miyagun kwayoyi ga matasa domin su rika aikata laifuka.
Shugaban hukumar reshen jihar Kano Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio, a wani bangare na magance matsalolin tu’ammali da miyagun kwayoyi musamman a lokutan bukukuwan sallah.
Abubakar Idris Ahmad ya kara da cewa, ‘bincikensu ya gano cewa kusan duk manyan laifukan da ake aikatawa na rashin Imani, yana da nasaba da shan miyagun kwayoyi’.
Ya kuma bukaci matasa da su ji tsoron Allah su dai na shan miyagun kwayoyi domin suna cutar da lafiyar su da kuma cutar da al’umma ta hanyar aikata muggan laifuka.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login